Hegerberg ta lashe kyautar gwarzuwar BBC

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ada Hegerberg ce ta lashe kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta BBC ta bana

'Yar wasan Olympique Lyon, Ada Hegerberg ce ta lashe kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta BBC ta bana.

Dubban mutane ne suka zabi 'yar wasan mai shekara 21 ta tawagar kwallon kafar Norway.

Mata 'yar wasan tawagar Brazil ce ta yi ta biyu, sai Christine Sinclair ta Canada ta yi ta uku a zaben.

Sauran 'yan wasa biyar da sunansu ya shiga takarar ta gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC sun hada da Hedvig Lindahl ta Sweden da kuma Melanie Behringer ta Jamus.