Everton na tattaunawa da Ramirez

Malaga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sandro mai shekara 21 ya taka rawa a Malaga, inda ya ci kwallo 14 a gasar La Liga

Kungiyar Everton na tattaunawa da Malaga domin daukar Sandro Ramirez a kokarin da Ronald Koeman ke yi wajen kara karfin kungiyar a badi.

Sandro mai shekara 21 ya taka rawa a Malaga, inda ya ci kwallo 14 a gasar La Liga da aka kammala wadda Real Madrid ta lashe kofin.

Ana alakanta cewar dan kwallon zai koma Atletico Madrid da taka-leda, amma hukuncin hana kungiyar sayen 'yan kwallo ya bai wa Everton damar cinikin dan wasan.

Haka kuma kociyan na Everton, Koeman yana son ya taya dan kwallon Ajax, Davy Klaassen.