Griezman ya tsawaita zamansa a Atletico

Atletico Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Griezman ya koma Atletico Madrid daga Real Madrid a shekarar 2014

Antoine Griezmann ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a Atletico Madrid zuwa shekara daya.

An yi ta rade-radin cewar dan kwallon mai shekara 26, zai koma Manchester United ne da murza-leda a badi.

Amma ya amince ya ci gaba da wasa a Atletico, bayan da aka ki soke hukuncin hana kungiyar sayen sabbin 'yan wasan kwallon kafa da Fifa ta hukuntata.

Atletico ba za ta dauki dan kwallo ba har zuwa watan Janairu, bayan da kotun daukaka kararrakin wasanni ta duniya ta ki dage hukuncin da Fifa ta yanke a watan Yunin 2016.

Griezman ya ci kwallo 26 a kakar da aka kammala, inda Atletico ta kare a mataki na uku a kan teburin da Real Madrid ta lashe kofin, Barcelona ta yi ta biyu.