Usain Bolt ya sha kaye a hannun Justin Gatlin a gasar 100m a London

Gatlin and Bolt Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gatlin ya lashe gasar 100m yayin da Bolt ya yi na uku

Justin Gatlin ya burge duniya inda ya yi wa zakaran tseren duniya Usain Bolt fintinkau a gasar 100m, kuma ya lashe lambar zinare.

An bar Bolt da tagulla a ranar da ya yi tserensa na karshe kafin yayi ritaya, inda Ba'amurke Christian Coleman mai shekara 21 yayi na biyu.

Duk da an lura cewa Usain Bolt yana samun 'yan matsaloli yayi da aka yi wasannin da suka gabata, amma yawancin mutane sun riga sun ba shi nasara a tseren da zai iya basa gwal na 20 da yayi nasara.

Ga yadda gasar ta kasance.

Hakkin mallakar hoto .

Kasar Amurka ce ta lashe zinare da azurfa, inda Jamaica ta yi na uku da na hudu.

A gasar Olympics ta shekarar 2004 a birnin Athens, Gatlin ya sha ihu daga 'yan kallo saboda a da, an taba kama shi har sau biyu yana amfani da wani haramtaccen maganin dake kara masa karfi.

Duk da cewa Usain Bolt bai yi nasara ba, amma 'yan kallo a filin wasan sun yi ta kiran sunansa, "Usain Bolt! Usain Bolt!."

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba