Neymar: 'Barcelona ta fi duk wani dan wasa'

Neymar da rigar PSG
Image caption Neymar ya ce ba ya je PSG ba ne domin ya zama tauraro

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya ce ba wani dan wasa da ya fi kungiyar, kwana hudu bayan sun sayar wa da Paris St-Germain Neymar, a kan kudin da ba a taba sayen wani dan wasa ba a duniya.

Neymar mai shekara 25, ya koma kungiyar zakarun Faransan a kan euro miliyan 222.

Bartomeu ya ce za su yi taka-tsantsan wurin kashe kudin da suka sayar da dan wasan na Brazil, ba da suna so ba.

Tafiyar Neymar daga Barcelonan ta kawo karshen annobar da suka zamarwa abokan karawa, tsakaninsa da kyaftin din Argentina Lionel Messi da dan wasa gaba na Uruguay Luis Suarez.

Dan wasan ya ci wa Barcelona kwallo 105 a kaka hudu da ya yi mata, inda ya dauki manyan kofuna bakwai, da suka hada da na Zakarun Turai guda daya da kuma na La Liga biyu.

Neymar ya ce ya koma Faransa ne domin fuskantar babban kalubale, amma ba wai kudi ne ya ji shi ba.

Yanzu dai ana rade-radin Barcelona na neman Philippe Coutinho, na Liverpool ko Ousmane Dembele na Borussia Dortmund ko Julian Draxler na PSG domin maye gurbin Neymar.