Tseren mita 100 : Mahaifin Gatlin ya bata rai kan ihu

Justin Gatlin Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Justin Gatlin a lokacin da ya yi nasara a tseren mita 100

Mahaifin zakaran tseren mita dari na duniya Justin Gatlin ya ce ihun da aka yi wa dansa lokacin da yake karbar lambar zinariya a gasar Landan cin mutunci ne ga wasan.

An yi wa Ba'amurke Gatlin, wanda ya aka yi wa hukuncin haramcin shiga tseren har sau biyu saboda amfani da abubuwan kara kuzari, ihu kafin da kuma bayan tseren karshe na gasar guje-guje da tsalle-tsalle a Landan, lokacin da aka ba shi lambar zinariyarsa.

Mahaifin nasa Willie Gatlin ya ce, ya yi hukuncin da aka yi masa na haramcin shiga wasan, sannan kuma ya manta da komai ya dage ya sake dawowa fili, ya yi abin da zai iya.

Gatlin, mai shekara 35, ya yi nasara ne a cikin dakika 9.92, inda ya doke dan uwansa Ba'amurke Christian Coleman a matsayi na biyu, yayin da gwarzon duniya, dan Jamaica Usain Bolt, ya zama na uku.

Bolt, mai shekara 30 ya kasa samun nasarar cin lambar zinariyarsa ta duniya ta 20 a wasansa na karshe na tseren mita 100, kafin ya yi ritaya.

A shekara ta 2001, aka fara dakatar da Gatlin tsawon shekara biyu, tun lokacin yana kwaleji, saboda amfani da wani magani da aka hana amfani da shi.

Amma ya yi nasarar kare kansa da cewa ya sha ne domin wata larura da ke damunsa, wanda kuma aka dage masa hukuncin ya dawo wasa bayan shekara daya.

Sannan a 2006 bayan ya yi nasara a tseren mita 100 da kuma na mita 200 a gasar duniya ta 2005 a Helsinki, bayan an yi masa gwaji an gano ya yi amfani da wani abin kara kuzarin.