Van Dijk ya nemi Southampton ta sayar shi

Virgil van Dijk Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun 2015 Virgil van Dijk ya koma Southampton

Kyaftin din Southampton Virgil van Dijk ya mika bukatarsa ta neman barin kungiyar, tare da cewa an ci mutuncinsa da aka ce yaki yin atisaye.

Kungiyoyi da dama na zawarcin dan wasan bayan dan Holland, kuma ya ce shi yana son tafiya Liverpool.

A watan Yuli kociyan Southampton din Mauricio Pellegrino ya ce ya bayar da umarni dan wasan ya yi atisaye shi kadai.

A takardar bukatar da ya mika, Van Dijk ya ce yana son kungiyar ta yi la'akari da zawarcinsa da manyan kungiyoyi suke yi, idan har yanzu da bukatar.

Ya ce maganar da kungiyar ta yi cewa shi ba na sayarwa ba ne, ta bata masa rai, kuma yadda kungiyar ke watsi da zawarcinsa da manyan kungiyoyi ke yi abin na ci gaba da ba shi takaici.

Van Dijk mai shekara 26, ya ce ya mika takardar bukatar barinsa kungiyar, bayan da ya ce Southampton na neman cin tararsa albashin sati biyu.