Damben Boksin: 'McGregor zai doke Mayweather'

Mayweather da McGregor a wani taron manema labarai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mayweather na ganin zai samu dala miliyan 300 a damben na ranar 26 ga watan Agusta

Ritayar shekara biyu da Floyd Mayweather ya yi daga damben boksin, za ta ba wa abokin karawarsa Conor McGregor damar kafa wani tarihi a damben da za su yi mai takaddama in ji tsohon zakaran duniya Carl Froch.

McGregor wanda dan damben hannu da kafa ne zai kara da Ba'amurke Mayweather, mai shekara 40, a Las Vegas ranar 26 ga watan Agusta,a damben da kowannensu zai iya samun dala miliyan 100.

Froch wanda tsohon zakaraun duniya ne na boksin na ajin matsakaita nauyi sau hudu ya gaya wa BBC Sport cewa: "kowa yana ganin Mayweather ne zai yi nasara a damben, to amma za a sha mamaki.

Ya ce jama'a za su ga sabanin haka saboda shekarar McGregor 29, matashi ne da ke cike da buri da kuma kwarin guiwa.

Froch dan Nottingham ya kara da cewa, ya kwana da sanin cewa McGregor ba dan damben boksin ba ne, dan damben hannu da kafa ne, to amma duk da haka zai bayar da mamaki tun a tashin farko-farkon damben.

A watan Yuli na 2015 ne Froch ya yi ritaya, wata 14 bayan ya doke George Groves ya rike kambinsa na WBA da IBF a filin wasa na Wembley.