'Ozil na son barin Arsenal, Hazard zai koma Barca'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ozil ya koma Arsenal ne a shekarar 2013 daga Madrid

Dan wasan tsakiyar kulob din Arsenal, Mesut Ozil, yana son barin kungiyar, kuma har ma ya fara shirye-shiryen komawa Barcelona, kamar yadda jaridar Daily Star Sunday ta ce.

Hakazalika, jaridar ta ruwaito cewa kungiyar Chelsea tana da aniyyar sayar da dan wasanta Eden Hazard ga Barcelona a kan fam miliyan 110.

Manchester United ta ce ba za ta sayar wa Tottenham Anthony Martial ba, in ji jaridarIndependent.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Martial mai shekara 22 ya koma Man U daga Monaco a shekarar 2015

Kocin Liverpool Jurgen Klopp yana neman dan wasan kungiyar Napoli, Lorenzo Insigne, idan Philippe Coutinho ya tafi Barcelona, kamar yadda jaridar Sunday People ta wallafa.

Ga alama kocin ya tsorata ne bayan jin labarin da jaridar Sunday Express ta wallafa, wanda ya ce Barcelona za ta kara taya Coutinho a kan fam miliyan 100.

Chelsea za ta kara gwada sa'arta kan zawarcin dan wasan Leicester City wato Danny Drinkwater, yanzu kungiyar ta taya shi ne a kan fam miliyan 25, a cewar Sunday Telegraph.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Drinkwater wanda tsohon dan wasan United ne, ya koma Leicester City ne a shekarar 2012

Real Madrid ta amsa cewa an kasa ta a zawarcin golan Manchester United David de Gea, in ji Sunday Express.

Jaridar Mail ta wallafa labarin da ke cewa Barcelona ta sayi tsohon dan wasan Tottenham, Paulinho a kan fam miliyan 36.6 daga kungiyar Guangzhou Evergrande ta kasar China.

Labarai masu alaka