West Bron ta ki sallama wa Man City Jonny Evans

West Brom Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Jonny Evans ya yi shekara tara yana taka-leda a Manchester United

West Brom ta ki sallama tayin da Manchester City ta yi wa dan wasanta Jonny Evans kan kudi fam miliyan 18.

An fahimci cewar tun a kwanakin baya ana tattaunawa kan batun daukar dan kwallon, amma kawo yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba.

Sauran shekara biyu yarjejeniyar Evans ta kare a West Brom wadda ya koma da taka mata leda daga Manchester United a 2015.

West Brom ta ki amince wa da tayin fam miliyan 10 da Leicester City ta yi wa dan wasan mai shekara 29.

Evans ya buga wa Manchester United wasa 198, kuma koci Louis van Gaal ne ya ce baya cikin 'yan wasan da zai yi amfani da shi a United.