Zidane ya ci kofi bakwai a Real Madrid

Zidane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kofi bakwai Zidane ya ci tun komawarsa Real Madrid da horar da tamaula

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya yi nasarar cin dukkan wasan karshe bakwai a gasa da ya jagoranci kungiyar.

Kocin ya fara da lashe Kofin Zakarun Turai, bayan da Real Madrid ta doke Atletico Madrid da ci 5-3 a bugun fenariti a San Siro ta Milan din Italiya bayan da suka tashi wasa 1-1 a kakar 2015/16.

Daga nan ne Zidane ya dauki kofi na biyu bayan da ya yi nasara a kan Sevilla a UEFA Super Cup da ci 3-2, sannan ya doke Kashima Antlers a Kofin Zakarun nahiyoyin duniya da ci 4-2 a dai kakar 2015/16.

Da aka shiga shekarar 2017 Real ta lashe kofin Zakarun Turai na 12 bayan da ta doke Juventus da ci 4-1, ta kuma ci Kofin La Liga na 2016/17 sannan ta doke Manchester United da ci 2-1 a UEFA Super Cup.

Kofi na bakwai da Zidane ya lashe shi ne Spanish Super Cup, bayan da ya yi nasarar cin Barcelona 5-1 gida da waje.