Swansea ta sayo 'yan wasa — Mourinho

Swansea Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karo na shida Mourinho ya ci Swansea da canjaras biyu a karawar da suka yi, kuma hudu a filin wasa na Liberty ya yi nasara

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya bai wa Swansea shawara cewar su sayo karin 'yan wasa a kudin da suka sayar da Gylfi Sigurdsson.

Swansea City ta sayar wa Everton, Gylfi Sigurdsson kan kudi fan miliyan 45, kuma shi ne dan kwallo na biyu mafi tsada da ya koma can, bayan Romelu Lukaku daga Chelsea.

Swansea na daf da sayen dan wasan Hull City mai buga wasan tsakiya Sam Clucas.

Bayan da Sigurdson ya bar kungiyar ne United ta doke Swansea 4-0 a wasan mako na biyu a gasar Premier a ranar Asabar.

A wasan makon farko ma United ta ci West Ham United 4-0, kuma rabaon da kungiyar ta ci wasa hudu ko sama da haka a farkon fara Premier tun shekara 110.

Labarai masu alaka