Samir Nasri ya koma Antalyaspor

Man City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nasri ya yi wa City wasa 129 tun komawarsa can daga Arsenal a 2011

Dan wasan Manchester City, Samir Nasri ya koma Antalyaspor ta Turkiya kan yarjejeniyar shekara biyu kan kudi fam miliyan 3.2.

Tun a yammacin Lahadi aka fitar da hoton Nasri mai shekara 30 zai shiga jirgin saman da zai kai shi Turkiya, domin a duba lafiyarsa.

Dan kwallon tawagar Faransa ya koma City daga Arsenal kan fam miliyan 25 a shekarar 2011, ya kuma buga wa City wasa 129.

Dan wasan ya ci kofin Premier biyu da FA da League Cup biyu a zaman da ya yi a Ettihad, amma a bara ya buga wasa aro a Sevilla ta Spaniya.

Nasri ya bi City wasannin atisayen da ta yi a Amurka, amma baya cikin 'yan wasan da Pep Guardiola ke son sawa a fafatawad da kungiyar za ta yi a bana ba.

Tsohon dan wasan Barcelona, Samuel Eto'o shi ne kyaftin din Antalyaspor