Messi baya son Coutinho ya koma Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Lionel Messi yana da rawar da yake takawa ta hana Philippe Coutinho zuwa Barcelona, domin baya son a cikin cinikin a hada da bai wa Liverpool Ivan Rakitic ko Serio Roberto in ji Don Balon.

L'Equipe ta ce Tottenham ta kusa kulla yarjejeniya da Paris St-Germain domin ta dauki Serge Aurier kan kudi fam miliyan 23.

Barcelona za ta sake taya Coutinho idan mahukuntanta sun ziyarci bikin raba jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai da ta Europa idan suka hadu da na Liverpool a ranar Alahamis in ji Mundo Deportivo.

Mail ta wallafa cewar Diego Costa yana son ya bar Chelsea ya sake komawa kungiyarsa Atletico Madrid.

Paris St-Germain na daf da amincewa ta dauki aron dan kwallon Monaco, Kylian Mbappe domin ya buga mata tamaula har zuwa karshen kakar bana in ji Sky Sports.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mbappe an yi ta rade-radin zai koma Real Madrid a bana

Barcelona ta fahimce cewar Liverpool ba za ta sayar mata da dan kwallon Brazil, Philippe Coutinho, mai shekara 25 a bana ba in ji Mirror.

Independent ta ce Barcelona ta hakikance cewar Lionel Messi da Andres Iniesta wadan da saura kaka daya yarjejeniyarsu ta kare a Camp Nou za su tsawaita zamansu.

The Sun ta ce Atletico Madrid ta bukaci Diego Costa cewar ya sasanta da Chelsea kafin su yi tunanin sayo shi daga Stamford Bridge domin a rabu lafiya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Conte ne ya ce ba zai yi amfani da Costa a wasannin bana ba

Manchester City za ta bar zawarcin dan wasan West Brom, Jonny Evans za ta koma neman Ben Gibson na Middlesbrough wanda za ta taya fam miliyan 20 in ji Independent.

Labarai masu alaka