Odey ne na daya a cin kwallo a Firimiyar Nigeria

Nigerian League Hakkin mallakar hoto LMCNPFL
Image caption Saura wasanni uku a kammala gasar Firimiyar Nigeria ta bana

Dan wasan Mountain of Fire Stephen Odey ne ke kan gaba a jerin 'yan wasan Firimiyar Nigeria da suka fi cin kwallaye a raga, inda yake da 18.

Anthony Okputo na Lobi Stars ne na biyu da kwallo 17, sai dan kwallon Abia Warriors, Sunday Adetunji mai 14 a raga a mataki na uku.

'Yan wasa biyar ne keda kwallaye sha bibiyu a raga da suka hada da Godwin Obaje da Alhassan Ibrahim da Samuel Mathias da Mfon Udoh da kuma Kingsley Eduwo.

Bayan da aka kammala wasannin mako na 35 a ranar Lahadi, har yanzu Plateau United ce ta daya da maki 62, Mountain of Fire ce ta biyu da maki 59, sai Akwa United ta uku da maki 54.