Tottenham ta sayi Serge Aurier daga PSG

Serge Aurier Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tottenham ta kammala sayen dan wasan baya na Paris St-Germain Serge Aurier kan fam miliyan 23.

Dan kwallon na Ivory Coast, mai shekara 24, ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar har zuwa 2022.

Batun samun izinin aiki ne ya kawo tsaiko a cinikin saboda hukuncin daurin je-ka-ka-gyra-halinka da aka yanke masa saboda cin zarafin dan sanda a bara.

"Wannan kamar wata sabuwar rayuwa ce a gare ni. A shirye nake na nuna kwarewa a ciki da wajen filin kwallo," a cewar Aurier.

"Magoya baya sun ne mafiya muhimmanci a kowanne kulob kuma a shirye nake na nuna musu cikakken Serge Aurier."

Aurier shi ne na hudu da Spurs ta saya a bana, bayan mai tsaron gida Paulo Gazzaniga da Juan Foyth da Davinson Sanchez.

Labarai masu alaka