Akwai ayar tambaya kan hukumar FFP — Wenger

da alama mun kirkiro dokokin da ba zamu iya mutuntasu ba. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption da alama mun kirkiro dokokin da ba zamu iya mutuntasu ba.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya yi tambaya dangane da ko ya kamata a rushe dokokin hukumar kula da kudaden da kulob-kulob ke kashewa wato FFP, inda ya ce kulob-kulob ba sa mutanta su.

A shekarar 2013 ne hukumar kwallon kafa ta Turai, FFP ta bayyana tsarin sarrafa kudaden da kowanne kulob ke kashewa su yi dai-dai da abin da kudadenta na shiga.

Ana binciken kungiyar Paris St-Germain bayan da ta biya fam miliyan 200 na sayen dan kwallon Brazil Neymar.

Wenger ya ce, "Da alama mun kirkiro dokokin da ba zamu iya mutunta su ba".

Labarai masu alaka