'Liverpool ba za ta daukaka kara ba kan jan katin Sadio Mane'

Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester City ta lallasa Liverpool da ci 5-0 ranar Asabar

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce ba za su daukaka kara ba kan jan katin da aka ba Sadio Mane inda ya ce "wani karin ba ta lokaci ne, kamar wasan da suka buga da Manchester City", in ji jaridar Independent.

Shi ma tsohon wasan Manchester United Rio Ferdinand ya nuna cewa ya sha aikata irin abin da Mane ya yi, amma ba a taba yi masa hukunci irin nasa ba, kamar yadda ya wallafa wani hoto a shafinsa na Twitter.

Hakkin mallakar hoto TWITTER

Arsenal ta amince da yarjejeniyar sayen Thomas Lemar daga Monaco a watan Janairu. Dan wasan Faransar zai kulla yarjejeniyar shekara biyar ne inda za a rika biyan fam 250,000 a kowane mako, in ji jaridar Daily Star.

Ita ma kungiyar Manchester United ta shirya neman Leymar, in ji jaridar Sunday Mirror.

Sabon dan wasan Leicester City, Adrien Silva, yana atisaye da kaninsa saboda yadda ba a yarda ya yi atisaye da sabuwar kungiyarsa ba yayin da bar kungiyar Sporting Lisbon, an ki amincewa ne saboda cinikinsa ya saba wa dokar hukumar Fifa, a cewar jaridar Leicester Mercury.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Silva ya koma Leicester City a kan fam miliyan 22 a ranar 31 ga watan Agustan bana

Kungiyar Juventus za ta yi zawarcin dan wasan Southampton Virgil van Dijk, a watan Janairu, kamar yadda jaridar Sunday Mirror ta wallafa.

Atletico Madrid ta tura wata tawaga Chelsea a ranar Asabar don kammala batun cinikin sayen Diego Costa daga Chelsean, a cewar jaridar Sunday Express.

Labarai masu alaka