Man United za kara da Basel a kofin Turai

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A bara United ta lashe kofin Europa League

Manchester United za ta karbi bakuncin Basel a wasan rukunin farko a gasar cin kofin Zakarun Turai ta 2017/18, kuma ita ce gasa ta 21 da kungiyar za ta fafata.

United ba ta samu shiga gasar da aka kare ba, wacce ta fafata a Europa League ta kuma cinye kofin, dalilin da ya sa ta samu gurbin shiga gasar bana.

Wannan ne karo na biyar da kungiyoyin biyu za su kara a gasar ta Zakarun Turai, inda suka yi canjaras a wasa biyu kowacce ta ci karawa daya.

United ce ke kan gaba a matsayin kungiyar Ingila da ta fi halartar gasar ta Turai, kuma ta hudu a nahiyar bayan Real Madrid da Barcelona da Porto.

Liverpool ce kungiyar Ingila da ta fi United cin kofin zakarun Turai wacce ta lashe sau biyar jumulla, ita kuwa United uku ne da ita.

Wannan ne karo na biyar da Mourinho ke jan ragamar kungiyoyi daban-daban zuwa gasar, bayan da ya kai Porto da Chelsea da Inter Milan da kuma Real Madrid wasannin.

Labarai masu alaka