Messi ya ci kwallo 301 a La Liga a Nou Camp

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ta hada maki 15 a wasa biyar da ta buga a gasar La Liga ta bana

Barcelona ta ci gaba da taka rawar gani a gasar La Liga, bayan da ta ci Eibar 6-1 a wasan mako na biyar da suka fafata a ranar Talata.

A karawar ce Lionel Messi ya ci kwallo hudu, sauran 'yan wasan da suka ci wa Barcelona sun hada da Paulinho da kuma Denis Suarez.

Eibar ta zare kwallo daya ta hannun Sergi Enrich a lokacin wasa ya koma 3-1.

Da wannan sakamakon Messi dan wasan tawagar Argentina ya ci kwallo tara a gasar La Liga, kuma guda 301 jumulla ya ci a Nou Camp a shekara 13 da ya yi a kungiyar.

Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta ci wasa biyar tana da maki 15.

Labarai masu alaka