Man U za ta fafata da CSKA Moscow ba 'yan wasanta uku

Man United za ta fafata da CSKA Moscow ba tare da 'yan wasanta uku ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Man United za ta fafata da CSKA Moscow ba tare da 'yan wasanta uku ba

Manchester United za ta fafata da CSKA Moscow a gasar zakarun Turai na ranar Laraba, inda za ta ziyarci kungiyar ba tare da Marouane Fellaini, dMichael Carrick da kuma Paul Pogba ba.

Fellaini ya yi rauni a wasan da suka kara da Southampton a makon jiya, inda suka yi nasara da ci 1-0.

Pogba bai taka leda ba tun bayan karawarsau da Basel inda suka yi nasara da ci 3-0.

Pogba bai taka leda ba tun bayan karawarsau da Basel inda suka yi nasara da ci 3-0.

Har'ila yau Carrick ma ya yi rauni, sai dai ana sa ran Phil Jones zai iya taka leda bayan dakatar da shi daga buga wasa a Turai.

United ta buga wasa takwas a bana ba tare da an doketa ba, ita kuwa CSKA ta yi nasara a wasanta na farko a rukunin A .

Labarai masu alaka