Zakarun Turai: Mourinho ya ce suna gab da kaiwa matakin gaba

Romelu Lukaku lokacin da yake cin kwallo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yanzu Lukaku ya ci wa Manchester United kwallo 10 a wasa tara

Jose Mourinho ya ce gab suke da kaiwa matakin sili-daya-kwale a gasar zakarun Turai bayan da Manchester United ta bi CSKA Moscow har gida ta casa ta da ci 4-0.

Kociyan ya ce duk da cewa wasa hudu ne yanzu a gabansu a rukunin, kasancewar sun fara da kyau, yana ganin kamar ma sun kai mataki na gaba na gasar.

A wasan na rukuni na daya (Group A), wanda aka yi ranar Laraba, Romelu Lukaku, ya ci biyu sannan Anthony Martial ya ci da fanareti, kafin Henrikh Mkhitaryan kuma ya ci ta hudu.

Mourinho ya ce abin da ke da muhimmanci shi ne a wasa biyu suna da maki shida, sannan kuma ga su da kyakkyawan matsayi a gasar, in ji kociyan wanda kungiyar tasa ta doke Basel 3-0 a wasansu na farko.

Da wannan sakamako, yanzu Lukaku ya ci kwallo 10 a wasa tara, tun lokacin da ya koma United daga Everton a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa da ta gabata.

Yanzu dai a tarihi ba a doke Man United ba a wasa shida a waje da wata kungiya ta Rasha.

'Yan wasan kungiyar ta Premier sun sanya rigarsu ta uku ne mai launin fatsa-fatsa, launin da rabonsu da sanyawa tun lokacin wasansu na Premier a gidan Southampton a watan Afrilu na 1996.

A wancan lokacin Southampton ta ci su 3-0 a kashin farko na wasan, abin da ya sa 'yan United din suka sauya rigar, saboda wai ba sa ganin junansu.

To amma a wannan wasan da CSKA ba su gamu da wannan matsala ba, inda suka kwashi garabasa a karawar ta gabashin Turai.

A daya wasan rukunin tsohon dan gaba na Norwich Ricky van Wolfswinkel ya ci da fanareti, a wasan da Basel ta casa Benfica 5-0.

Manchester United ce ta daya a rukunin da maki shida, sai Basel da maki uku, yayin da CSKA mai maki uku ita ma take zaman ta uku, amma da bashin kwallo biyu, Benfica tana ta karshe ba maki ko daya.