Man City ta doke Chelsea har gida

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A minti na 67 ne De Bruyne ya samu nasarar jefa kwallo a gasar Chelsea

Manchester City ta doke Chelsea da ci 1-0 a gasar firimiya da suka yi ranar Asabar a filin wasa na Stamford Bridge.

Ita ma takwararta Manchester United ta samu nasara a kan Crystal Palace da ci 4-0.

Yanzu United da City suna kankankan a gasar, sai dai City ce take saman tebur da bambancin kwallaye, yayin da United take biye mata.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka fafata a gasar kamar haka:

  • Huddersfield 0-4 Tottenham
  • Bournemouth 0-0 Leicester
  • Man Utd 4 -0 Crystal Palace
  • Stoke City 2-1 Southampton
  • West Brom 2 -2 Watford
  • West Ham 1 -0 Swansea

Pogba zai yi doguwar jinya – Mourinho

Aguero ya karya kashin hakarkari

Labarai masu alaka