Andres Iniesta: Zai ci gaba da zama a Barca har abada

Lionel Messi celebrates with Barcelona team-mate Andres Iniesta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Andres Iniesta ya lashe kofuna 30 tare da Barcelona

Kyatin din Barcelona Andres Iniesta ya sanya hannu a yarjejeniyar zama a kungiyar har abada.

Dan wasan kasar Spain din ya yi wa Barcelona wasa sau 639 wanda shi ne na biyu a jerin tarihin 'yan wasan da suka fi taka wa kungiyar teda, inda ya yi nasarar zura kwallaye 55 a raga.

Iniesta ya je kungiyar ne a shekarar 1996 lokacin da yake da shekara 12 da haihuwa.

Ya fara taka leda ne a watan Oktobar shekarar 2002, kuma ya yi nasarar lashe Kofin Zakarun turai har sau hudu.

Dan wasan gaban ya zama kyatin din kungiyar ne a shekarar 2015 kuma kofuna 30 ya lashe a tarihin zamansa a kungiyar, kamar dai takwaransa Lionel Messi.

A wata sanarwa da Barcelona ta fitar ta ce: "Andres Iniesta ya sanya hannu a yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar har karshen rayuwarsa ta kwallon kafa a ranar Juma'a."

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba