Nigeria da Zambia: Kun san gwarzon dan wasan?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sai dai kuma Shehu Abdullahi mai sanye da riga lamba 12 ya samu katin gargadi a wasan

Dan wasan Super Eagles, Shehu Aabdullahi, da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Anorthosis Famagusta ta kasar Cyprus, shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a karawar Supera Eagles din Najeriya da Chipolopolo na Zambiya da maraicen Asabar.

Baya ga kasancewa wanda ya bai wa Alex Iwobi kwallon da ya ci bayan hutun rabin lokaci, an zabi Shehu Abdullahin ne a matsayin gwarzon dan wasa domin irin kariyar da ya bayar a bayan Najeriya ta dama da kuma farmakin da ya yi ta kaiwa gidan Zambiya.

An bai wa dan wasan kyautan kudi naira miliyan daya tare da buhuhunan shinkafa domin gudumawar da ya bayar a wasan.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, dan wasan da ya buga wasa a Kuwait kafin ya koma Cyprus, ya taya 'yan Najeriya murnar samun shiga cikin jerin kasashen da za su fafata a gasar kwallon kafa ta duniya a Rasha cikin shekarar 2018.

Shehu Abdullahi dai ya bar Kano Pillars zuwa kungiyar kwallon kafa ta Qadsia SC da ke Kuwait ne a shekarar 2014.

Amman a shekarar 2015 dan wasan dan asalin Sakkwato ya koma kungiyar kwallon kafa ta C.F. Uniao da ke Portugal.

A shekarar 2016 Shehu Abdullahi ya koma kungiyar da yake taka wa leda yanzu a Cyprus.

Abdullahi ya fara buga wa Super Eagles din Najeriya kwallo ne a shekarar 2014 lokacin da ya buga wasanni a gasar cin kofin Afirka da aka yi a watan Janairun shekarar.

Labarai masu alaka