Gareth Bale baya cikin 'yan takarar Ballon d'Or

Ballon d'Or Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bale ya ci kwallo biyar a Real Madrid a bana, yana kuma fama da rauni

Dan kwallon tawagar Wales da Real Madrid, Gareth Bale baya cikin 'yan takarar fitatcen dan kwallon da yafi yin fice a duniya ta Ballon d'Or ta bana.

Shi kuwa Harry Kane na Tottenham dan wasan tawagar Ingila shi ne daya tilo daga Ingila da yake cikin 'yan takara ta bana mai murza-leda a gasar Premier.

Sauran 'yan kwallon da suke takara masu wasa a Premier sun hada da David de Gea da Philippe Coutinho da Sadio Mane da Kevin de Bruyne da N'Golo Kante da kuma Eden Hazard.

Cikin 'yan wasa 30 da mujallar kwallon kafa ta Faransa ta fitar har da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da Neymar, sai dai babu Gareth Bale dan kwallon tawagar Wales da Real Madrid.

Ronaldo ne ya lashe kyautar bara karo na hudu, bayan da ya doke Messi mai rike da lambar yabon karo biyar.

Ga 'yan wasa 30 da ka bayyana sunayen su:

 1. Pierre-Emerick Aubameyang (Borussia Dortmund da Gabon)
 2. Karim Benzema (Real Madrid da France)
 3. Leonardo Bonucci (AC Milan da Italy)
 4. Gianluigi Buffon (Juventus da Italy)
 5. Edinson Cavani (Paris St-Germain da Uruguay)
 6. Philippe Coutinho (Liverpool da Brazil)
 7. Kevin de Bruyne (Manchester City da Belgium)
 8. David de Gea (Manchester United da Spain)
 9. Paulo Dybala (Juventus da Argentina)
 10. Edin Dzeko (Roma da Bosnia-Herzegovina)
 11. Radamel Falcao (Monaco da Colombia)
 12. Antoine Griezmann (Atletico Madrid da France)
 13. Eden Hazard (Chelsea da Belgium)
 14. Mats Hummels (Bayern Munich da Germany)
 15. Isco (Real Madrid da Spain)
 16. Harry Kane (Tottenham da England)
 17. N'Golo Kante (Chelsea da France)
 18. Toni Kroos (Real Madrid da Germany)
 19. Robert Lewandowski (Bayern Munich da Poland)
 20. Sadio Mane (Liverpool da Senegal)
 21. Marcelo (Real Madrid da Brazil)
 22. Kylian Mbappe (Paris St-Germain ada France)
 23. Dries Mertens (Napoli da Belgium)
 24. Lionel Messi (Barcelona da Argentina)
 25. Luka Modric (Real Madrid da Croatia)
 26. Neymar (Paris St-Germain da Brazil)
 27. Jan Oblak (Atletico Madrid da Slovenia)
 28. Sergio Ramos (Real Madrid da Spain)
 29. Cristiano Ronaldo (Real Madrid da Portugal)
 30. Luis Suarez (Barcelona da Uruguay)

Labarai masu alaka