Kante da Morata ba za su yi wa Chelsea wasa ba

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea mai rike da kofin Premier tana ta hudu a kan teburi da maki 13

'Yan wasan Chelsea, N'Golo Kante da Alvaro Morata ba za su buga mata gasar Premier da za ta fafata da Crystal Palace a ranar Asabar ba.

Chelsea na son sanin girman raunin da Kante ya yi a lokacin da yake yi wa Faransa tamaula da Bulgeria a wasan shiga gasar cin kofin duniya.

Sai dai Chelsea ta ce raunin da Morata ya yi a lokacin da ta fafata da Manchester City bai kai girman da ta za ta tun farko ba.

Chelsea za kuma ta kara da Roma a wasan cikin rukuni a gasar cin kofin Zakjarun Turai a ranar 18 ga watan Oktoba.

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya ce watakila ya yi amfani da Eden Hazard a matsayin lamba tara.

Labarai masu alaka