Kwana 500 tun bayan da Madrid ta ci Kofin Turai na 11

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ta ci Kofin Zakarun Turai guda 12 jumulla

Yau shekara daya da wata hudu da kwana 10 ke nan, wato a takaice, kwana 500 cif tun bayan da Real Madrid ta lashe Kofin Zakarun Turai na 11 a birnin Milan na Italiya.

Kuma shi ne Kofin Turai na biyu da kungiyar ta lashe a cikin shekara uku, kuma na farko da sabon koci Zinedine Zidane ya ci wa Madrid.

Real ta buga wasan karshe ne da Atletico Madrid a ranar 28 ga watan Mayun 2016 a filin wasa na Giuseppe Meazza da ke Italiya.

Sai da wasan ya kai bugun fenariti, inda dan kwallon Atletico Juan Fran ya barar, shi kuwa Cristiano Ronaldo ya ci wa Madrid kwallon da ya ba ta damar cin Kofin a karo na 11.

Daga nan ne Real ta sake daukar Kofin Zakarun Turai na biyu a jere kuma a karo na farko da ta yi hakan tun bayan da aka sauya masa fasali.

Cikin wadannan kwana 500 Zidane ya ci European Super Cup biyu da Super Copa de Espana da kofin Zakarun nahiyoyin duniya da La Liga da kuma Kofin Zakarun Turai biyu.

Labarai masu alaka