An nada Figo mai bayar da shawara a UEFA

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Luis Figo tsohon dan wasan Barcelona da Real Madrid ne

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA ta nada tsohon dan wasan tawagar Portugal, Luis Figo a matsayin wanda zai dunga ba ta shawara a fagen kwallon kafa.

Figo zai bi sahun Nadine Kessler da kuma Dejan Stankovic wadanda a shekarar bara hukumar kwallon kafar Turai ta ba su aikin ba ta shawara.

Kuma dukkansu za su yi aiki kafada da kafada da shugaban UEFA, Aleksander Ceferin da kuma sashin wasan tamaula.

Haka kuma za su yi aikin zakulo tsare-tsaren kwallon kafa don ci gaba a nahiyar da duba kan hukunce-hukunce tamaula da yadda mutane za su kara son kwallon kafa a nahiyar.

Figo daya ne daga cikin 'yan takarar shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya a 2015.

Labarai masu alaka