Dan wasan Arsenal, Mustafi, zai yi jinyar mako shida

Mustafi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mustafi ya fice daga wasan karshe na neman shiga gasar cin kofin duniya da Jamus ta buga ne da dingishi

Dan wasan bayan Arsenal, Shkodran Mustafi, ba zai buga wa kungiyar kwallon kafar wasa ba na mako shida bayan ya ji ciwo acinya, in ji kociyan Gunners Arsene Wenger says.

Dan wasan dan asalin Jamus mai shekara 25 ya fice daga fili ne da dingishi bayan ya ji ciwo kafin a ba da hutun rabin lokaci a wasan da kasar mai rike da kofin kwallon kafa na duniya ta kammala wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya dinta da nasarori ta hanyar lallasa Azerbaijan 5-1 ranar Lahadi.

"Za mu rasa Mustafi na tsawon mako hudu ko shida," in ji kociyan Gunners, Arsene Wenger.

"Ba na tunanin zai iya buga mana wasa kafin a sake ba da hutun bai wa 'yan wasan damar taka wa kasashensu leda."