Zakarun Afirka:TP Mazembe sun gamu da jinkirin komawa kasarsu

Wasu magoya bayan TP Mazembe Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Dubban magoya bayan TP Mazembe ne ake sa ran za su tarbi kungiyar bayan ta dauki Confederation Cup ranar Asabar a Afirka ta Kudu

Zakarun Confederation Cup na Afirka, TP Mazembe, na DR Congo sun gamu da cikas ta jinkirin jirgin saman da zai koma da su gida, Lubumbashi, bayan da suka sake daukar kofin a jere, daga Afirka ta Kudu.

'Yan Mezemben sun yi canjaras da 'yan SuperSport United na Afirka ta Kudu a karawa ta biyu da suka yi ranar Asabar, a Pretoria, abin da ya ba su damar rike kofin bayan sakamako 2-1 jumulla wasa gida da waje.

A ranar Litinin din nan ya kamata su koma gida birnin Lubumbashi na Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo amma suka gamu da matsala da jirginsu.

Sai dai mai kungiyar wanda kuma shi ne jagoran 'yan hammayya a kasar ta Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo, Moise Katumbi, ya yi zargin cewa, hukumomin zirga-zirgar jiragen sama na Congon ne suka ki ba wa jirgin izinin sauka idan ya taso.

To amma zuwa yanzu babu wani bayani na hukuma kan dalilin jinkirin jirgin 'yan wasan.

Kofin na Confederation shi ne na hudu na Afirka da kungiyar ta TP Mazembe ta dauka a cikin shekara uku.