Sakamakon Premier: Man City ta sha da kyar 2-1 da Southampton

Raheem Sterling lokacin da ya ci Southampton Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Cin shi ne na tara da Raheem Sterling ya yi a Premier bana

Raheem Sterling ya ceci Manchester City bayan da ya ci mata bal a cikin dakika talatin ta karshen wasansu da Southampton, aka tashi 2-1, inda nasarar ta zamar musu ta 12 a jere a Premier.

Tun da farko De Bruyne ne ya ci wa Manchester City kwallo a minti na 47 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, kafin kuma Romeu ya rama wa bakin a minti na 75.

Bayan minti 90 ana fafatawa 1-1, alkalin wasa ya kara minti biyar na lokacin da aka bata, wanda a cikin dakika 30 ta karshen lokacin ne Sterling ya sheko kwallon a murde ba ta tsaya ko ina ba sai a ragar Southampton, fili ya rude da sowa.

Yanzu Manchester City ta kara tazarar da ke tsakaninta da Manchester United ta biyu a tebur zuwa maki takwas, yayin da ita Southampton ta zama ta 11 da maki 16 a tebur.

Sakamakon sauran wasannin Premier na Laraba;

Arsenal 5-0 Huddersfierd ; Arsenal tana matsayi na 4 da maki 28, yayin da Huddersfield take ta 14 da maki 15.

Bournemouth 1-2 Burnley ; Bournemouth tana ta 15 da maki 14, yayin da Burnley take ta 6 da maki 25.

Chelsea 1-0 Swansea ; Chelsea tana ta 3 da maki 29, Swansea tana matsayi na 19 da maki 9.

Everton 4-0 West Ham ; Everton ta zama ta 13 da maki 15, West Ham na matsayi na 18 da maki 10.

Stoke City 0-3 Liverpool ; Stoke na matsayi na 16 da maki 13, ita kuwa Liverpool na matsayi na biyar da maki 26.