Kofin Europa: Sam Allardyce ba zai jagoranci Everton ba

Sam Allardyce da Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Everton ce kungiyar Premier ta bakwai da Sam Allardyce ya yi wa kociya

Kociyan Everton Sam Allardyce ba zai halarci wasan kofin Europa da kungiyarsa za ta yi da Apollon Limassol ba a Cyprus ranar Alhamis, saboda zai gana da likitansa.

A ranar 30 ga watan Nuwamba aka nada Allardyce, mai shekara 63, domin maye gurbin Ronald Koeman, kuma kawo yanzu wasan kawai da ya jagoranci kungiyar shi ne na Premier wanda ta doke Huddersfield 2-0 ranar Asabar.

Jami'an horar da manyan 'yan wasan kungiyar Craig Shakespeare da Duncan Ferguson, su ne za su jagorance ta a wasan na kofin Europa, inda take ta karshe a rukuninsu na biyar (Group E), wanda ba za ta iya kaiwa mataki na gaba ba na kungiyoyi 32.

An doke Everton din sau hudu a wasanta biyar da ta yi na rukuni-rukuni na gasar ta Europa, kuma ranar Lahadi za ta fuskanci Liverpool a wasan hamayya na Merseyside na Premier ranar Lahadi.