Manny Pacquiao: Sanata, Dan dambe, Soja, Mawaki, Dan fim, Kociya duk shi kadai

Manny Pacquiao da wasu hafsoshin sojin kasar Philippines Hakkin mallakar hoto MANNY PACQUIAO
Image caption Manny Pacquiao a tsakiya bayan samun karin girma a rundunar sojan kasa ta Philippines

Idan da akwai wani hatsabibin dan wasa mai komai da ruwanka a zamanin nan to za a iya cewa shi ne tsohon zakaran damben duniya na ajin nauyi har takwas, Manny Pacquiao.

Shi dai Pacquiao dan kasar Philippines mai shekara 38, bayan fagen da duniya ta fi saninsa na damben boksin, dan siyasa ne, wanda a yanzu haka yake zaman dan majalisar dattawa a kasar.

Bayan wannan mawaki ne, sannan ba a bar shi a baya ba a fagen yin fina-finai domin tauraron fim ne, sannan kuma ya taba kasancewa mai horar da 'yan wasan kwallon kwando na kasar.

To a yanzu kuma likkafar Manny Pacquiao ta kara yin gaba, bayan da ya samu karin girma a matsayinsa na sojan kasar ta Philippines me zaman ko-ta-kwana, inda ya ci jarrabawar karin girma daga mukamin laftana kanar, zuwa kanar.

A watan Yuli ne Pacquiao ya rasa kambin boksin dinsa na ajin matsakaita nauyi na hukumar boksin ta duniya, WBO, a karawarsa da dan kasar Australia Jeff Horn wanda ya ba da mamaki a damben.