Zakarun Turai: Tottenham ta kafa tarihi bayan doke Apoel 3-0

Fernando Llorente na Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fernando Llorente ya ci ya kuma bayar an ci a wasan zakarun Turai a karon farko a wasansa

A karon farko Fernando Llorente ya ci wa Tottenham kwallo a wasansa na 17 a kungiyar ta Mauricio Pochettino, wadda ta kammala wasanta na rukuni na takwas (Group H) da nasara 3-0 a kan Apoel, ta kai zagayen kungiyoyi 16 gasar.

Tun kafin wasan na Laraba daman kungiyar ta zama ta daya a rukunin, abin da ya sa ta hutar da wasu daga cikin fitattun 'yan wasanta ta jarraba wasu.

Llorente, wanda Tottenham ta sayo daga Swansea, ya daga ragar ne a minti na 20 da shiga fili, kafin Son Heung-min ya biyo baya minti 17 tsakani, sai kuma can a minti na 80 Nkoudou ya ci ta uku.

Tottenham, ta zama kungiyar da ta kammala wasan rukuni na gasar ta zakarun Turai ta bana da mafi yawan maki, 16.

Yanzu kuma za ta yi kokarin kawo karshen wasa hudu da ta yi ba tare da nasara ba a gasar Premier idan ta karbi bakuncin Stoke ranar Asabar da karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya.