Zidane ya lashe kyautar koci da babu kamarsa

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Real Madrid tana ta hudu a kan teburin La Liga

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya lashe kyautar kocin Faransa da ya fi taka rawa a shekarar 2017, wanda French magazine ta bayyana.

Zidane ya lashe kofin Zakarun Turai da na La Liga da Uefa Super Cup da Spanish Cup da na Zakarun nahiyoyin Duniya a 2017.

Wannan ne karo na biyu da mujallar ta sanar da kocin a matsayin dan Faransa da babu wanda ya kai shi taka rawa.

Sai dai kuma Real Madrid tana fama da kalubale a kakar bana, inda take ta hudu a kan teburin La Liga, wanda Barcelona wadda ke mataki na daya ta ba ta tazarar maki 16.

Sai dai kuma Real za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai wasan zagaye na biyu da Paris St Germain a watan Fabrairu, kuma tana cikin gasar Copa del Rey.

Labarai masu alaka