Everton za ta dauki Theo Walcott

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Walcott ya ci wa Arsenal kwallo 108 tun lokacin da ya koma can da murza-leda a 2006

Likitocin Everton na daf da duba lafiyar Theo Walcott, a shirin da take na daukarsa daga Arsenal kan fam miliyan 20.

Alamu na nuna cewar Walcott mai shekara 28, ya gama buga wa Arsenal tamaula, wadda ya koma can daga Southampton shekara 12 da suka wuce.

Dan wasan ya ci kwallo 108 a wasa 397 da ya buga wa Gunners, amma daga baya Arsene Wenger baya saka shi a wasa akai-akai.

Idan har cinikin ya fada, Arsenal za ta yi amfani da kudin wajen sayo dan kwallon Borussia Dortmund, Pirre-Emerick Aubameyang da dan wasan Bordeaux Malcom.

Haka kuma Arsenal tana son daukar dan kwallon Manchester United, Henrick Mkhtariyan, inda take son ta sayar wa da United Alexis Sanchez.

Labarai masu alaka