Plateau ta hada maki shida a wasa biyu a Firimiya

Mai rike da kofin Premier Nigeria, Plateau United ta hada maki uku, bayan da ta ci Rivers United 2-0 a wasan mako na biyu da suka kara a ranar Laraba.
Plateu United ta fara cin kwallo ta hannun kyaftin dinta Elisha Golbe a bugun tazara, sannan ta ci na biyu ta hannun Emeka Umeh.
Plateu United wadda ta ci Nasarawa United daya mai ban haushi a ranar Lahadi, ta hada maki shida kenan a wasa biyu da ta buga.
Ita ma kuwa Kano Pillars 2-0 ta doke Nasarawa United, inda Junior Lokosa ya ci kwallo ta hannun Junior Lokosa da kuma Alassan Ibrahim.
Ga sakamakon wasannin mako na biyu da aka buga:
- MFM 1-0 Kwara
- Yobe Stars 2-0 Wikki
- Rangers 1-2 Lobi
- El-Kanemi 1-0 Abia Warriors
- Sunshine 2-1 Katsina
- Go Round 1-0 Akwa
- Tornadoes 2-1 FCIU
- Enyimba 0-0 Heartland