Man Utd ta kai wasan karshe bayan doke Tottenham 2-1

'Yan wasan Manchester United na murnar kaiwa wasan karshe na FA Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United ta kai wasan karshe na cin kofin cikin gida (Ingila) a karo na 29, fiye da kowa ce kungiya a Ingila

Ander Herrera ya ci wa Manchester United bal din da ta sa ta kafa tarihin zuwa wasan karshe na cin kofin FA a karo na 20, tare da fitar da Tottenham a gasar a wannan mataki karo na takwas a jere, da ci 2-1.

Tottenham ta fara wasan ba kakkautawa abin da ya sa ta shiga gaban United minti 11 da bal din da Dele Alli ya zura.

Kungiyar ta Jose Mourinho ta jure hare-haren har hakarta ta cimma ruwa a minti na 24, bayan da Alexis Sanchez ya farke da ka da wata bal da Paul Pogba ya aika masa, wadda ta kasance ta takwas da ya ci a filin na Wembley a wasansa na takwas a can.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rabon da Tottenham ta yi nasara a wasan kusa da karshe na kofin FA tun 1991

Can a minti na 62 ne Herrera ya ci wa Manchester United bal din da ta kai kungiyar wasan karshe da za ta yi tsakanin wadda ta yi galaba a karawar ranar Lahadi ta Chelsea da Southampton, ran 19 ga watan Mayu.

Rashin nasarar ya sa Pochettino ya yi kaka hudu ke nan a Tottenham ba tare da ya ci kofi ba.