Kalli hotunan 'yan wasan Madrid da suka fafata da Bayern Munich

Tawagar 'yan wasan Real Madrid sun iya birnin Munich na Jamus domin karawa da Bayern Munich a wasan farko na dab da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Wannan ne karo na 25 da kungiyoyin biyu za su fafata a gasar Turai.

Mun zabo muku wasu daga cikin hotunan 'yan wasan na Madrid lokacin da suka isa Jamus:

Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Kusan dukkan 'yan wasan Real Madrid sun tafi domin wannan wasa
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Ciki har da Toni Kroos wanda tsohon dan wasan Bayern Munich ne
Image caption Gareth Bale na cikin tawagar, wacce ta isa Munich a ranar Talata
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption A bara ma Madrid ce ta fitar da Bayern a zagayen dab da na kusa da na karshe
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Magoya baya sun fita domin yin maraba ga tawagar ta Madrid
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Kyaftin Sergio Ramos, wanda bai buga wasa na biyu da Juventus ba, na cikin tawagar a wannan karon
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Cristiano Ronaldo (daga dama) ya ci kwallo a duk wasan da ya buga a gasar a bana. Yana tare da Marcelo (tsakiya) da Casemiro (daga hagu)
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Bayern Munich ta fitar da Sevilla a zagayen da ya gabaci wannan
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Yayin da Real ta doke Juventus da kyar a zagayen dab da na kusa da na karshe

Labarai masu alaka