Ba ni na sayar da Mohamed Salah ba - Jose Mourinho

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mohamed Salah ya ci kwallaye 31 a wasa 33 a gasar Firimiya ta bana

Jose Mourinho ya ce ba shi ya yanke shawarar sayar da dan wasan gaban Masar, Mohamed Salah ba, a lokacin da yake kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Salah, mai shekara 25, ya bar Stamford Bridge zuwa Roma a shekarar 2016 kuma kawo yanzu ya ci kwallaye 43 a cikin dukkan wasannin da ya buga wa Liverpool tun da ya koma kungiyar a farkon kakar wasa ta bana.

Mourinho, wanda a yanzu shi ne kocin Manchester United, ya ce Chelsea ta sayar da dan wasan ne domin ta sami kudin sayan wasu 'yan kwallon.

Dan kasar Portugal din ya shaida wa kafar watsa labarai ta ESPN cewar: "Mutane suna cewa ni ne na sayar da Salah kuma gaskiyar lamarin ba haka ya ke ba".

"Chelsea ce ta yanke shawarar sayar da shi. Saboda haka, mun yanke shawarar bayar da aron shi tare ne, amma bayan hakan shawarar sayar da shi domin sayan wasu 'yan wasan ba tawa ba ce."

Da aka tambaye shi game da lamarin a taron manema labaran da ya shirya a ranar Juma'a, Mourinho ya kara da cewa: "Kowa ya san ni na sayi Salah; ni ke da alhakin hakan (sayanshi).

"Na sayi dan matashin dan wasa da ya iya murza-leda. Mun yanke shawara tare da shi cewar ya fi masa kyau ya je ya buga wasan aro na wani lokaci."

Salah ya koma Chelsea ne a karkashin Mourinho a shekarar 2014, amma an bayar da aronsa ga Fiorentina sa'annan ga Roma kafin ya koma kungiyar kwallon kafa ta Italiyar gaba daya kan kudi fam miliyan 15.

Bayan ya koma gasar Firimiya ta hanyar a Liverpool, Salah ya ci kwallaye 31 a cikin wasanni 33 kuma ya ci kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na kwararrun 'yan wasa.