Bam ya hallaka mutum 25 a a Afghanistan

Wasu mata da wani hari ya hada da 'yan uwansu a Afghanistan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A baya bayan nan kungiyar IS na daukar alhakin hare-haren da ake kaiwa a Afghanistan

Akalla mutum 25 ne suka mutu ciki har da dan jaridar kamfanin AFP a wasu hare-haren bam na kunar-bakin wake da aka kai a yankin da ma'aikatar tsaro da tattara bayanan sirri da kuma NATO suke, a babban birnin Afghanistan, Kabul.

Dukkanin hare-haren biyu an kai su ne a yankin Shashdarak na birnin inda ma'aikatar tsaro da ta tattara bayanan sirii da kuma ofisoshin kungiyar tsaro ta NATO suke.

Dan kunar bakin-wake ne a kan babur ya kai harin farko, amma hari na biyu wanda bam din ya tashi a wurin na farko lokacin da mutane suka tattaru domin taimako da ganin abin da ya faru, ba a san wanda ya kai shi ba, wanda.

Wani dan jarida na kamfanin AFP wanda yake daukar hoto a lokacin da bam din na farko ya tashi na daga wadanda suka mutu a na biyun.