Burtaniya: Amber Rudd ta yi murabus daga sakatariyar harkokin cikin gida

Sakatariyar harkokin cikin gidan Burtaniya da ta yi Amber Rudd Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sakatariyar harkokin cikin gidan Burtaniya ta fuskanci suka kan yaudara

Sakatariyar harkokin cikin gida ta Burtaniya, Amber Rudd, ta yi murabus bayan shafe makonni tana fuskantar matsin-lamba a kan batun fitar da 'yan ci-ranin da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

A wasikar barin aikinta, Ms Rudd ta amsa cewa lallai ta yaudari majalisa a kan batun.

Wasu takardu da aka bankado sun nuna yadda ta yi kokarin kara adadin yawan 'yan ci-ranin da ake shirin kora, duk da cewa ta musanta aikata hakan.

'Yan ci-ranin yankin Caribbean wadanda suka shafe shekaru aru-aru a Burtaniya, su suka fi fuskantar wannan barazanar.

Murabus din Ms Rudd ya daga wa Theresa May hankali sosai, saboda alama ce ta rashin dai-daituwar gwamnati da koma baya, 'yan kwanaki kafin a gudanar da zaben kananan hukumomi.

Jam'iyyar hamayya ta Labour Party, ta bukaci Fra minista Theresa May ta yi bayani, a kan ko ta san irin abubuwan da Ms Rudd ke aikatawa na yaudara.

A martanin da ta mayar, Fra ministar ta ce Ms Rudd ta bayar da hujojji daidai gwargwado da zuciya guda, kuma ta fahimci dalilan ajiye aikin da ta yi domin ta dau alhakin kuskuren da aka samu.

Ms Rudd ita ce mutum na hudu da ke murabus din tilas a gwamantin May cikin watani shida bayan Sir Micheal Fallon da Priti Patel da Damian Green. Shi ma James Brokenshire ya ajiye aiki saboda dalilan lafiyarsa.

Labarai masu alaka