An dakatar da lafarin Najeriya Joseph Ogabor saboda 'cuwa-cuwa'

Alamar CAF Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwamitin alkalan wasa na CAF ya tabbatar da hukuncin da kwamitin da'a na hukumar ya yanke na dakatar da Joseph Ogabor

Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta dakatar da alkalin wasa Joseph Ogabor na Najeriya saboda ya yi "kokarin karkata sakamako".

CAF ta ce lamarin ya faru ne a wasan da aka buga tsakanin kulob din Plateau United na Najeriya da USM Alger na Aljeriya a gasar cin kofin zakarun Afirka na Confederation Cup ranar 7 ga watan Afrilu a Legas.

"Matakin ya biyo bayan bincike da kuma shaidun da jami'an da suka kula da wasan da Afirka ta Kudu suka gabatar, wadanda Ogabor ya tuntuba domin neman su tallafawa kulob din na Najeriya," a sanarwar CAF.

An kuma gargadi Plateau United "da su daina bai wa jami'an wasa kyaututtuka wadanda akan iya yi wa kallon wani yunkuri na cin hanci."

A wani lamarin mai alaka da wannan, sanarwar ta ce "an nemi Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka ta Kudu ta nemi afuwar takwararta ta Najeriya (NFF) bayan bincike ya nuna cewa babu wata shaida da ta nuna wani jami'in NFF na da hannu a zargin ba da toshiyar baki na dala 30,000".

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba