'Yan wasan Arsenal da za su kara da Atletico Madrid

'Yan wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Arsenal

'Yan wasan Arsenal sun yi atisayen karshe kafin su bar London domin tafiya birnin Madrid inda za su kara da Atletico a wasan dab da na karshe na gasar Europa.

An tashi 1-1 a wasan farko da kungiyoyin biyu suka buga a filin wasa na Emirates.

A ranar Alhami ne kuma za a yi karawa ta biyu a Wanda Metropolitano gidan Atletico Madrid.

Wannan wasan shi ne dama ta karshe da ta rage wa Arsenal ta cin kofi a bana da kuma zuwa gasar zakarun Turai ta badi.

Kuma ita ce gasar nahiyar Turai ta karshe da koci Arsene Wenger zai jagoranci Arsenal bayan ya bayyana zai bar kungiyar a karshen kaka.

Samun nasarar lashe kofin Europa zai yi tasiri sosai ga sabon kocin da zai gaji Wenger saboda gasar zakarun Turai musamman wajen zubin sabbin 'yan wasa

Ga wasu daga cikin hotunan 'yan wasan da za su buga wasan:

Hakkin mallakar hoto Arsenal
Hakkin mallakar hoto Arsenal
Hakkin mallakar hoto Arsenal
Hakkin mallakar hoto Arsenal
Hakkin mallakar hoto Arsenal
Hakkin mallakar hoto Arsenal
Hakkin mallakar hoto Arsenal
Hakkin mallakar hoto Arsenal

Labarai masu alaka