Damben Audu Argungu da Dogon Bahagon Sisco
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Damben Audu Argungu da Dogon Bahagon Sisco

Sakamakon wasannin damben gargajiya da aka yi a safiyar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Mohammed Abdu ne ya hada rahotan

Damben da aka yi kisa:

 • Autan Bahagon Maru daga Arewa ya buge Garkuwan Dangero Guramada,.
 • Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu ya yi nasara a kan Bahagon Ali Kwarin Ganuwa daga Arewa.
 • Tetenus din Na Bacirawa daga Arewa ya buge Garkuwan Dangero Guramada.
 • Dan Yalo Autan Sikido daga Kudu ya doke Shagon Idi Guramada.
 • Dunan Dangero Guramada ya buge Shagon Abata Mai daga Kudu.
 • Garkuwan Bahagon Alin Tarara daga Arewa ya buge Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu.

Wasannin da aka yi canjaras:

 • Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da Garkuwan Bahagon Alin Tarara daga Arewa.
 • Bahagon Audu Argungu daga Arewa da Dogon Washa Guramada.
 • Autan Fafa daga Arewa da Shagon Faya daga Kudu.
 • Dogon Bahagon Sisco daga Kudu da Bahagon Audu Argungu daga Arewa.
 • Carkin Dan Rijau daga Aewa da Dogon Bahagon Sisco daga Kudu

Labarai masu alaka