Hoton Ozil da Erdogan ya bar baya da kura

Mesut Özil and President Erdogan, 13 May 18 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mesut Özil (daga hagu) ya bai wa Shugaba Erdogan kyautar rigarsa ta Arsenal

Hukumar Kwallon Kafar kasar Jamus (DFB) ta soki yadda dan wasan Arsenal Mesut Özil da kuma Ilkay Gündogan na Man City suka dauki hoto tare da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Duka 'yan wasan biyu wadanda aka haifa a kasar Jamus kuma suke da asali a Turkiyya, sun bai wa Mista Erdogan kyautar riguna wasansu a Landan ranar Lahadi.

Gündogan ya rubuta: "Ga shugabana mai daraja, wanda nake girmamawa."

Mista Erdogan yana neman kara tsayawa a zaben shugaban kasar.

Özil da Gündogan duka suna shirye-shiryen taka leda ne a Gasar Cin Kofin Duniya wadda za a fara watan Yuni a kasar Rasha.

Sai dai kasar Turkiyya ba ta samu damar zuwa gasar ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasa ukun wadanda 'yan asalin Turkiyya ne (Ilkay Gündogan na Man City da Mesut Özil na Arsenal da kuma Cenk Tosun na Everton sun dauki hoto da Mista Erdogan

'Yan siyasar Jamus da dama sun soki 'yan wasan, inda suke sa alamar tambaya game ga biyayyarsu ga akidojin dimokradiyyar Jamus.

Shugaban Hukumar DFB Reinhard Grindel ya ce: "Kwallon Kafa da Hukumar DFB suna da wadansu akidojin wadanda Mista Erdogan ba ya mutuntawa.

"Saboda haka bai kamata 'yan wasanmu su bari a yi amfani da su wajen kamfen din siyasa. Abin da 'yan wasan suka yi, bai taimaka wa hukumar DFB ba wajen hadin kan jama'a."

A lokacin da yake matashi a shekarun 1990, Mista Erdogan ya taba taka leda a kungiyar Kasimpasa wadda take birnin Istanbul.

Labarai masu alaka