Sam Allardyce zai zama kocin Ingila

Sam Allardyce Hakkin mallakar hoto z
Image caption Sam Allardyce ya taka rawar gani a Sunderland

A ranar Alhamis ne ake sa ran Ingila za ta nada Sam Allardyce a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafar kasar.

Zai bar kungiyar Sunderland inda ya shafe watanni tara yana horas da tamola.

Allardyce ya maye gurbin Roy Hodgson, wanda ya yi murabus a watan Juni bayan da Iceland ta fitar da Ingila a zagaye na biyu na gasar Euro 2016.

Kocin mai shekaru 61, wanda ya taba horas da West Ham, Newcastle, Bolton da kuma Notss County, ya tattauna da hukamar kwallon kasar.

An zabe shi ne a kan kociyan Hull City Steve Bruce wanda shi ma ya nemi aikin.

Abin da ya rage yanzu shi ne cimma matsaya kan diyyar da za a biya Sunderland, domin Allardyce yana da ragowar shekara daya a kwantiraginsa a kulob din.