Steve Bruce ya bar Hull City

Steve Bruce Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Steve Bruce ya taka rawar gani a Hull City

Steve Bruce ya raba-gari da kungiyar Hull City bayan da ya taimakawa kulob din ya dawo gasar Premier a bana.

Kocin mai shekaru 55, wanda bai halarci atisayi a safiyar Juma'a ba, ya fada a baya cewa ba shi da tabbas kan makomarsa a kungiyar.

Bruce ya zamo kociyan Hull ne a shekarar 2012, inda ya dawo da su Premier a bana daga gasar Championship.

A wannan makon ne Bruce ya gana da Hukumar Kwallon Kafa ta FA kan yiwuwar zamowa kocin Ingila, aikin da ake sa ran Sam Allardyce zai samu.

Masu sharhi na ganin Bruce na kan gaba a sahun wadanda za su iya maye gurbin Allardyce a Sunderland, idan har ya bar kulob din.

Labarai masu alaka