Rasha ta sha kasa a kotu kan gasar Olympics

Yelena Isinbayeva Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yelena Isinbayeva na cikin 'yan wasan da suka shigar da karar

Kotun koli da ke kula da harkokin wasanni ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa 'yan wasan guje-guje na Rasha daga shiga gasar wasanni ta Olympics saboda zargin amfani da kwayoyi masu kara kuzari.

Hukumar kula da guje-guje (IAAF) ce ta dakatar da 'yan wasan kasar bayan da wani rahoto na musamman ya same su da laifin amfani da miyagun kwayoyi a matakai daban daban.

Kwamitin gasar Olympics na Rasha da wasu 'yan wasa 68 sun daukaka kara kan matakin, inda kotun ta saurari shaidu daga bangarorin biyu.

Daga nan ne kuma ta yanke hukuncin cewa dakatarwar na nan daram.

A wani lamarin na daban kuma, Hukumar Kula da Wasannin Olympics ta duniya na duba yiwuwar dakatar da 'yan wasan kasar baki daya daga gasar.

Hakan ya biyo bayan wani rahoto daban da na farko wanda ya bankado yadda hukumomi ke daurewa 'yan wasa gindi su yi amfani da kwayoyin da aka haramta.

Hukumar Kula da Guje-guje ta IAAF ta yi marhabin da hukuncin na kotun da ke kasar Switzerland.

Kotun ta tabbatar da cewa Rasha ba za ta iya tura 'yan wasan guje-guje ba zuwa gasar Olympics da za a fara a watan Agusta a Brazil.

Labarai masu alaka